Kotu ta dakatar da umurnin shugaban kasar Guatamala
WASHINGTON DC —
Wata kotu a kasar Guatemala ta dakatar da umurnin Shugaban wannan kasa ta yankin tsakiyar nahiyar Amurka, na korar shugaban wata hukumar MDD ta yaki da cin hanci da rashawa, wadda ke binciken yadda kwamitin yakin neman zabensa ke samun kudaden gudanarwa.
Kotun Kundin Tsarin Mulki ta umurci gwamnatin kasar da kar ta aiwatar da umurnin Shugaba Jimmy Morales na tasa keyar Ivan Velasquez, wanda dan kasar Colombia ne. Jami'in na MDD ya yi kokarin binciken zargin biyan wani kudi ba bisa ka'ida ba da ake alakantawa da jam'iyyar shugaban, ta NCF.
A wani faifan bidiyon da aka saka a yanar internet jiya Lahadi, Morales ya ce ya kamata a kori Velasquez "saboda a kare muradun mutanen Guatemala, a karfafa doka da oda da kuma madafun iko."