Gwamnatin Koriya ta Kudu ta musanta rahotannin da ke cewa Shugaban Koriya ta Arewa Kim Jong Un ba shi da lafiya sosai bayan da aka yi masa aikin tiyata a zuciya.
"Babu wani abinda zai tabbatar mana da cewa Kim Jong Un ba shi da lafiya," wani babban jami'in ma'aikatar harkokin wajen Koriya ta Kudu ya fada wa Muryar Amurka.
Wani mai magana da yawun shugaban Koriya ta Kudu ya ce Seoul ba ta ga wani abu na ba-sabam dake faruwa a Koriya ta Arewa ba kuma babu wani “abu da zata tabbatar” game da Kim, wanda bai samu damar halartar wani muhimmin taron jama'a da aka yi a makon da ya gabata a kasar ba.
Jaridar Daily NK, ta Koriya ta Kudu wadda ake wallafawa ta yanar gizo da kuma wasu kafofi a Koriya ta Arewa, a ranar Talata 21 ga watan Afrilu sun bada rahoton cewa Kim yana samun sauki bayan tiyata da aka yi masa a zuciya.