Koriya ta Arewa Zata Yi Gwajin Makamin Nukiliya a Tekun Pacific Nan Gaba

Shugaban Koriya ta Arewa Kim Jong Un

Duk da karin takunkumi da Majalisar Dinkin Duniya ta yiwa kasar Koriya ta Arewa bisa gwaje gwajen makamai masu linzami da ta dinga yi da kuma ca da kasashen duniya suka yi mata, shugaban kasar ya ce nan ba da dadewa ba za ta gwada makamin nukiliya kan tekun pacific.

Koriya ta Arewa ta bayyana cewa mai yiwuwa ne nan ba da dadewa ba tayi gwajin wani makamin nukiliya a tekun pacific bayanda shugaban kasar Kim Jong Un yayi gargadi da cewa zai maida martanin barazanar shugaban Amurka da kuma sabbbin takunkumin da aka kakabawa kasar da takala.

Bisa ga kamfanin dillancin labaran Yonhap. Ministan harkokin kasashen ketare Ri Yong Ho ya shaidawa manema labarai cewa, gwajin makamin, maida martani ne da kasarsa zata yi sabili da barazanar da shugaban Amurka Donald Trump ya yi a jawabinsa ga taron kolin MDD farkon makon nan da cewa za a yi raga-raga da gwamnatin Koriya ta Arewa.

Kalaman Ministan harkokin kasashen ketaren da yayi a wata hira yayin wani taro a MDD, yazo ne ‘yan sa’oi bayanda shugaban Koriya ta Arewa Kim Jong Un yace Trump zai yabawa aya zaki sabili da barazanar da yake yi. Ri Yong Ho yace, mai yiwuwa ne kasarsa ta maida martani ta wajen gwada wani makamin nukiliya mai karbi a tekun Pacific.

Tilas ne irin wannan gwajin ya bi ta kan kasar Japan.

Kasar Koriya ta Arewa tayi gwajin makamin nukiliyanta na shida kuma mafi girma farkon wannan watan, amma tana gwajin dukan makamanta na nukiliya ne a wata cibiya ta karkashin kasa.