Koriya Ta Arewa Za Ta Hana Amurka Shiga Batun Nukiliyar Kasarta

Wannan kalaman na Kwon Jong Gun sun fito sa’o’i bayan da gwamnatin ta kaddamar da wani sabon shirrin gwajin makami mai linzami wanda suka kira "jigon dabarar makamai," wanda ya nuna karfin sojojin na Pyongyang.

Koriya ta Arewa, ta bukaci cewar kada Sakataren Harkokin Wajen Amurka, Mike Pompeo, ya sake shiga tattaunawar da ta shafi ayyukanta na nukiliya.

Kwon Jong Gun, wani babban jami'in ma'aikatar harkokin wajen Koriya ta Arewa, ya ce Pyongyang ta na son wanda ya kasance "mai hankali da kuma iya Magana cikin mutuntawa", a cewar wani rahoto daga jami'an kamfanin dillancin labarai na Koriya ta Arewa-KCNA.

Wannan kalaman na Kwon Jong Gun, sun fito sa’o’i bayan da gwamnatin ta kaddamar da wani sabon shirrin gwajin makami mai linzami wanda suka kira "jigon dabarar makamai," wanda ya nuna karfin sojojin na Pyongyang.

Kamfanin dillancin labarai na KCNA, ya ce Kim Jong Un, ya jagoranci gwaje-gwajen jiya Laraba, ya kuma kira shi "aiki mai mahimmanci."