Koriya Ta Arewa Ta Sake Harba Makaman Kare Dangi

Da safiyar yau Alhamis, Koriya ta Arewa, ta harba wasu makamai, masu linzami, masu tafiyar gajeren zango guda biyu, a gabashin gabar tekun kasar Korea ta Kudu. Ta ce abunda ke nuna cewa Pyongyang, na amfani da wannan matakin ne, ta kara samun karfi a tattaunawar da ta ke yi da Amurka game da batun makaman nukiliyarta.

Kwamitin sulhun Koriya ta Kudu, ya tabbatar da cewa, Korea ta Arewa ta harba wasu "sabbin makami masu linzami dake cin gajeren zango," a cewar wani sako zuwa ga ‘yan jarida, daga fadar Blue House ta shugaban kasar Koriya ta kudun, kwamitin sulhun, ya bayyana damuwa sosai akan harba makaman, yana mai cewa, matakin ba zai rage takaddamar soja ba.

An harba makaman masu linzami ne a wajen birnin Wonsan, da ke gabashin Korea ta Arewa, wadanda aka cilla, zuwa gabashin yankin, kafin makaman su fada cikin teku, a cewar rundunar sojojin Koriya ta Kudu. Rundunar ta kara da cewa, makami mai linzami na farko, ya yi gudun kimanin kilomita 430, sannan na biyun kuma, ya yi gudun kilomita dari 690.