A wani al'amari da ka iya farfado da tankiyar Amurka da Koriya Ta Arewa, Shugaba Kim Jong Un ya ba da umurnin gudanar da gwajegwajen muggan makamai, wanda hakan ya saba ma wata yarjejjeniyar da aka cimma.
WASHINGTON D.C. —
Kafar labaran gwamnatin kasar Koriya Ta Arewa ta tabbatar jiya Asabar cewa Koriya Ta Arewa ta yi gwaje-gwajen makamai masu linzami, wanda wannan ne karon farko da Koriya Ta Arewar ta ce wani abu kan gwaje-gwajen a hukumance, wanda kuma ke tayar da jijiyoyin wuya ta fuskar soji.
Kafar labaran ta gwamnatin Koriya Ta Arewa ta ce Shugaba Kim Jong Un da kansa ne ya bayar da umurnin a cilla rokokin ciki teku daga gabar gabashin kasar.
Hotunan da aka buga a kafafen yada labaran gwamnatin Koriya Ta Arewa na nuna Shugaba Kim na leka cikin tabaron hango nesa, sannan ya yi murmushi yayin da ya ke nuna allon bidiyon na’urar cilla makamin, lokacin da makamin ya dira kan wani tsibiri.