Koriya Ta Arewa Ta Janye Ofishin Huldar Ta Da Koriya Ta Kudu

A yau Jumma’a ne Koriya ta arewa ta sanar da makwabciyar ta koriya ta kudu akan matakin da ta dauka kwastam na janye ofishin a wurin taron kasashen biyu na mako-mako da suke yi a ofishin hadin gwiwar su dake arewacin birnin Kaesong.

Mukaddashin Ministan hadin kan koriya ta kudu Chun Hae-sun ya fadawa kamfanin dillancin labaran Reuters cewa koriya ta arewa ta ce daga koli aka bada umurnin daukar wannan matakin.

A wata sanarwa, Koriya ta kudu ta fadi cewa matakin da koriya ta arewa ta dauka na janyewa daga ofishin “bai dace ba,” amma sanarwar ta ce koriyar ta kudu zata ci gaba da aiki a ofisoshin.

Labarin janye ofishin na zuwa ne bayan lalacewar ganawar shugaban koriya ta arewa Kim Jong Un da shugaban Amurka Donald Trump a Vietnam cikin watan da ya gabata.