Koriya Ta Arewa Ta Ja Kunnen Koriya Ta Kudu Da Amurka

Wannan hoton da ma'aikatar tsaron Koriya ta Kudu ta bayar ya nuna wata bindigar igwa samfurin K-9 155mm tana maida martani ta hanyar bude wuta kan Koriya ta Arewa daga tsibirin Yeonpyeong.

Hukumomi a Pyongyang sun ce shirin atusayen soja da kasashen biyu keyi na gusawa da yankin ga fadawa cikin yaki gadan-gadan

A yau jumma'a Koriya ta Arewa ta yi gargadin cewa atusayen sojojin ruwa da Amurka da koriya ta Kudu suke shirin gudanarwa yana jefa yankin cikin kasadar fadawa yaki gadan-gadan.

Kamfanin dillancin labarai na Koriya ta Arewa yace atusayen da zai kunshi wani jirgin ruwan yakin Amurka mai jigilar jiragen sama, wanda kuma yake aiki da makamashin nukiliya, wani shiri ne na ganganci na masu kada gangar yaki a kan kasar Koriya ta Arewa. A can baya, Koriya ta Arewa ta yi amfani da irin wadannan kalamun wajen yin tur da atusayen soja a Koriya ta Kudu.

Cacar-baki da hura hanci na baya-bayan nan su na zuwa a daidai lokacin da shugaba Lee Myung-bak na Koriya ta Kudu yake duba jerin sunayen mutanen da zasu maye gurbin ministan tsaro, Kim Tae-young, wanda yayi murabus jiya alhamis bayan da aka zarge shi da laifin mayar da martani maras karfi a bayan harin da Koriya ta Arewa ta kai kan wani tsibiri na Kudu.

Sojoji biyu na Koriya ta Kudu da fararen hula biyu sun mutu, yayin da wasu mutanen su akalla 18 suka ji raunuka a wannan hari da Koriya ta Arewa ta kai kan tsibirin Yeonpyeong a kusa da bakin iyakar da suke rikici kai a cikin tekun Yellow Sea.