Da safiyar yau Litinin Koriya Ta Arewa ta harba makamai masu linzami guda hudu, uku daga cikinsu sun yi tafiyar kilomita dubu daya kamin su fada cikin teku, kilomita 350 kacal daga Japan, kamar yadda jami'an Koriya Ta Kudu da Japan suka yi bayani.
WASHINGTON, DC —
Sai dai da wuya ace gwajin na yau makamai ne masu cin dogon zango, da ake kira intercontinental Ballistic Missile da turanci.
Gwaji data yi yau ta gudanar da shi ne daga yankin kasar da ake kira Tongchang-ri kusa da kan iyakarta da China, inji rundunar sojojin koriya ta kudu.
Rundunar sojojin Amurka ta fada jiya Lahadi cewa ta gano kuma ya bai sawun gwajin makami mai linzami da Koriya Ta Arewa tayi, ta kara d a cewa gwajin bai yi barazana ga nahiyar Amurka ta arewa ba.
A bara, Koriya Ta Arewa ta zafafa gwajin makamai da take yi, inda tayi gwaje-gwaje daban daban fiyeda 25, na makamai masu linzami da kuma na Nukiliya biyu.