Sakataren Harkokin Wajen Amurka Rex Tillerson ya ce da Amurka da China na jin nauyi ya rataya a wuyansu game da batun Koriya Ta Arewa, Wadda jiya Lahadi ta yi gwajin wani babban makamin roka, wanda ta kira "sabon haihuwa" a bangaren makamanta na roka.
WASHINGTON D.C —
Damuwar da ake kan Koriya ta Arewa da kuma dada barazanar da take yi, su ne suka mamaye zance a ziyarar Tillerson, ta farko a yankin, inda ya yada zango a Japan da Koriya ta Kudu da kuma China, ta karshe a jerin wuraren da ya je.
Gwamnatin Donald Trump, na duba wata sabuwar hanyar bullo ma wannan al'amarin, kuma ta na neman yadda za ta hada kai da China wajen sa ido kan wurare masu sarkakkiya a yankin.
"Mun himmantu wajen yin duk abin da mu ke iyawa don kau da duk wani rikicin da ke iya barkewa. Kuma mun lura cewa akwai wasu matakan da za mu iya dauka wadanda sanannu ne ma gare mu," a cewar Tillerson, yayin da ya ke magana a wani taron manema labarai na hadin gwiwa da Ministan Harkokin Wajen China.