Kamfanin dillacin labaran kasar Koriya ta Arewa ya fitar da wata sanarwa ta sukan lamirin kasar China kai tsaye wadda ba a saba gani ba, yana bada misali da kalaman kamfanin dillancin labaran kasar China, yana kuma gargadin cewa kada kasar China ta kure hakurin Koriya ta Arewan.
WASHINGTON, DC —
“Kamata yayi China tayi nazarin abinda ka iya biyo bayan gangancin kokarin lalata dagan takar da ke tsakanin ta da Koriya ta Arewa, a cewar sanarwar da kanfanin dillacin labaran Koriya ta Arewa ya fidda jiya laraba.
Sanarwar ta ce kiran da China tayi akan Koriya ta Arewa ta yi watsi da shirin ta na makaman nukiliya ya wuce gona da iri kuma ya sabawa Koriya ta Arewan.
China dai tayi wadannan kalaman ne a jaridar Global Times ta kasar a yau Alhamis.
Jaridar ta kara da cewa, China ta ce ba zata yarda Koriya ta Arewa ta lalata mata bakin iyakar ta da ayyukan makamanta ba.