Koriya Ta Arewa Na Neman Tsara Dangantaka Ne da Sabuwar Gwamnatin Trump

Shugaban Koriya ta Arewa Kim Jong Un

Jami'ai a Koriya ta Kudu, sun ce sun hakikance barazanar da Koriya ta Arewa tayi a baya bayan nan cewa, zata harba makami mai linzami mai cin dogon zango,tayi ne da nufin tsara wata dangantaka da sabuwar gwamnatin Amurka ta Donald Trump.

Kakakin ma'aikatar sake hade zirin kiryan biyu, yace "da dagewa kan matsayarta na ci gaba da harba makamai masu linzamin, da kuma yin tsokana, hanya ce ta neman ganin Amurka ta sauya hallayarta gameda kasar ta Koriya ta Arewa. Jami'in yayi magana ne kwana daya bayan da Koriya ta Arewa tayi ikirarin cewa a shirye take ta harba makamai masu lainzami daga ko ina, kuma ako wani lokaci.

A Washington, sakataren tsaron Amurka Ash Carter, ya fada ranar Lahadi cewa, a Shirye Amurka take ta harbo duk wani makamimai lanizami wanda ya ratsa huruminta, ko na kawayenta ne.