Wata sanarwar da aka bayar a gidan telebijin na kasar ta ambaci Cibiyar Binciken Makamin Nukiliya ta kasar tana tabbatar da samun nasarar gwajin nukiliya da aka yi domin tantance yadda za a iya hada kundun nukiliyar da za a iya aza shi kan makamai masu linzami.
Mai karanta sanarwar ya ce gwajin makamin nukiliyar, wani bangare ne na martani ga barazana daga Amurka da sauran abokan gaba da ke yin ko oho da matsayin Koriya ta Arewa a zaman wadda ta mallaki nukiliya.
Hukumomi a Pyongyang basu sanar da duniya aniyarsu ta yin gwajin kafin su gudanar da shi ba.
Wannan rana ta 9 ga watan Satumba ita ce ranar cikar shekaru 68 da kafa kasar Koriya ta Arewa, kuma a can baya, kasar ta kan gudanar da gwaje gwajen nukiliya ko na makamai masu linzami a muhimman ranaku irin wannan.
Kasashen duniya sun yi tur da wannan gwajin, wanda aka ce shine mafi karfi na nukiliya da Koriya ta Arewa ta taba gudanarwa.