Maaikatar harkokin wajen kasar Korea ta Arewa ta kira takunkumin baya-bayan nan da MDD tasa mata wannan tamkar tana kada gangan yaki ne.
Tace domin haka yana nufin kulle harkokin tattalin arzikin kasar dungurungun.
A cikin wata sanarwan dake dauke a labaran kanfanin dillacin labarai na kasar KCNA data fitar.
Mai Magana da yawun maaikatar yace Pyongyang, kai tsaye tasa kafa tayi fatali da wannan kudiri.
Tace wannan kudirin ba kome bane illa sakamakon rawar da Amurka ke takawa na game da nasarar da Koriyan take samu wajen sarrafa shirin ta na makamin nukiliya.
A ranar jumaan data gabata ne dai kwamitin tsaro na MDD ya amince da ya sake kakaba wani zagayen takunkunmi ga Korea ta Arewan.
Takunkunmin dai ya auna bangaren ta na mai dama na shirin ta na makamai.
A cikin sanarwan da kasar ta Korea ta Arewa ta fitar yau lahadi ta kalubalanci Amurka.
Tana cewa idan har tana son ta zauna lafiya to ta jingine manufofin ta masu gauni kana ta koyi zama cikin ‘yan uwanta kasashen duniya musammam wadanda suka mallaki makamin nukiliya.
Haka uma kasar ta Korea ta arewa ta gargadi duk wata kasa data goyi bayan wannan kudiri to ta kuka da kanta akan duk wani abu da ya same ta, domin ko zata tabbatar kasar nan ta dandana kudar ta.