An umarci matasa da kada su dogara ga neman aikin gwamnati kwai wai domin sun yin karatun Boko kuma suna ganin cewa suna da digiri.
Wata matashiya kuma daliba a jami’ar kimiyya da fasaha ta Wudil dake Kanon Nijeriya Zainab Ibrahim, wace ta bayana haka ta ce duk lokacin da suka je dogon hutun makaranta tana kama sana’ar hannu ne gadan-gadan.
Ta bayyana haka ne yayin da take zantawa da DandalinVOA tana mai cewa lokacin da ake jiran gwamnati domin ta samarda aiki ya fara wuce wa.
Ta ce tana sana’ar dinki ne a cikin gida inda ‘yan uwanta mata ke kawo mata tana dinkawa, ta kara da cewa da sana’ar nata take dogo da kai wajen sayan littatafai da kasidu na makaranta.
Ta ce sana’ar dinkita yana rufa mata asiri, ta ce mussamam ma a lokacin Sallah da watan azumin Ramadan tana samun dinki har sai ta nemi wadanda zasu taimaka mata.
Zainab ta ce babban burinta shine ta bud katafaren shago inda zata kawata sana’ar tata a zamanance cikin tsari.
Ta ja hankalin ‘yan uwanta mata da su jajirce wajen neman nasu na kansu ko ba komai zasu rufawa kansu asiri a harkokin yau da kullum.