Mai baiwa shugaban ‘kasa shawara kan harkokin siyasa Sanata Babafemi Ojudu, yace sun lura da cewa wasu ‘yan ‘gaza gani’ sun dage sai sun shiga tsakanin shugaban Buhari da mataimakinsa, bayan kuwa shugaban da mataimakinsa duk abu ‘daya ne.
Kwararre kan sha’anin aikin gwamnati ‘Dan Masanin Fika, yace dalilin da yasa ake ganin abubuwa na faruwa ta hannun Osinbajo, saboda a baya su biyu ne kowa yana yin aikinsa, yanzu kuwa baki ‘daya ayyukan suna hannun Osinbajo domin Buhari baya nan. Ya kuma ‘kara da cewa wannan lamari ne na siyasa domin su nuna cewa yafi maigidansa kazar-kazar.
Sai dai kuma ‘dan jaridar da ya fara takalo wannan muhawara Mohammad bin Ibrahim, bai gamsu da duk ire-iren bayanan da kusoshin gwamnatin ke yi ba. inda ma yake ganin Buhari ba zai iya yin kazar-kazar din da Osinbajo yake yi a yanzu ba, haka zalika umarnin da mataimakin yake bayarwa irin wanda ya baiwa babban bankin kasar don karya darajar dalar Amurka.
Domin karin bayani saurari rahotan Hassan Maina Kaina.
Your browser doesn’t support HTML5