Kokarin Gwamnatin Najeriya Wajan Neman 'Yan matan Chibok

Buni Yadi bayan kisan daliban sakandire.

Kokarin da gwannatin Najeriya keyi domin neman 'yan matan Chibok da kuma matsayinta agame da cika kwanaki dari da kisan daliban Buni Yadi

A makon da ya wuce aka cika shekara guda da kinsan gillar da aka yi ma wasu daliban makarantar akandire a garin Buni Yadi amma kuma a wannan ranar ne shugaban kasar Najeriya Goodluck Jonathan ya tafi jahar Sokoto wajan bikin zagayowar cika shekara tasa'in na tsohon shugaban kasa Alhaji Shehu Shagari. Tambayar da wakilin sashin Hausa Bello Galadanci yayi wa kakakin gwamnatin Najeryar Mr Mike Omeri kenan inda shi kuma yace

"Akwai abubuwa da yawa da akayi wadanda ba daidai ba kuma wannan bukin ba na gwamnati bane, bikin da kawai zamuyi shine nasara akan samun kawo karshen kashe-kashen da ke faruwa na 'yan ta'adda da ke faruwa a kasar a yanzu. Idan muka rage wannan to lallai zamuyi babban biki. kuma abin damuwa koda mutum daya ne ya rasa ransa kamar yadda wadannan yara suka rasa rayukansu".

Kakakin gwamnatin ya kara da cewar suna nan suna kan neman 'yan matan Chibok kamar yadda wakilinn sashen hausar ya kara tambayar shi, ya kuma ce yanzu akwai sojojin makwabtan kasashe da kuma sauran kananan garuruwan da ke sa ido akan neman 'yan matan chibok, ya kara da cewar da Najeriya kadai ke neman su amma yanzu akwai hadin hannun sauran kasashe makwabta.

Daga karshe yayi kira ga iyayen yaran da abin ya shafa da cewar haryanzu dai suyi hakuri kuma har yanzu a dukkan masallatai da coci-coci 'yan Najerya masu son juna na yi masu addu'oi har zuwa lokacin da za'a sami nasara

Your browser doesn’t support HTML5

Buni Yadi


.