Kiddiga ta nuna akwai kimanin mutane miliyan 45 ke gudanar da rayuwar su a yankin tapkin Chadi wanda ya ratsa kasashen Najeriya, Nijer Kamaru da kuma Chadi.
Galibin mutanen dai sun dogara ne da albarkatun tapkin ta hanyar noma da kiwo da kuma uwa uba kamun kifi.
Ofishin kula da ayyukan jin kai na majalisar dinkin duniya dake Najeriya ya ce kimanin mutane miliyan 7 na fuskantar barazanar yunwa saboda dagulewar al’amura a lardin.
Shugaba Muhammad Buhari a babban taron Majalisar Dinkin Duniya makon jiya ya yi tsokaci kan yadda canjin yanayi ya taka rawa wajen kafewar tapkin da kuma irin kalubalen da kasashen dake makwaftaka suke fuskanta
Gabanin kalaman shugaba Buhari a zauren Majalisar Dinkin Duniyar kan wannan batu, ya yi makamantan su a yayin taron kasa da kasa da aka yi a Abuja cikin watan Fabrairun bana wadda hukumar kula da tapkin Chadi ta shirya da hadin gwiwa da gwamnatin tarayya da kuma hukumar Majalisar Dinkin Duniya ta UNESCO.
A makon jiya-ma masana sun karawa juna ilimi kan hanyoyin bunkasa noma a yankuna masu fama da karancin ruwan sama, wadda cibiyar nazarin harkokin noma a wurare masu kamfar ta jami’ar Bayero ta shirya.
Batun kalubalen tapkin Chadi na daga cikin abubuwan da suka mamaye ajandar taron.
Farfesa Tijjani Alu Adamu na jami’ar Abdumumini dake Yamai a Jamhuriyar Nijar, masanin kimiyyar harkokin noma ne kuma ya gabatar da Makala a zauren taron.
Bayan da Farfesan ya ba da dalilan da suka haddasa kafewar tapkin. Yace Allah ya fitar da wata kasa mai albarka a yankin idan an yi shuka kanta sai cimaka ta fito saboda niimar dake karkashin kasar. Sanadiyar hakan mutane da dama sun koma yankin tapkin sun dukufa da noma. Amma yanzu idan an kawo ruwa da zummar farfado da tapkin kasar da take da albarka ruwa binneta zai yi. Farfesa Adamu yace ga miliyoyin mutanen da suke zauna a yankin suna noma idan kasar da suka dogara akai babu ita, to wata sabuwar matsala ta taso.
Masu kula da lamura dai na ganin cewa, tilas sai an hada karfi da karfe tsakanin kwararru da mahukunta kafin a iya warware kalubalen da wannan lardi na tapkin Chadi ke fuskanta.
A saurari rahoton Mahmud Ibrahim Kwari
Your browser doesn’t support HTML5