Kofin Duniya: Najeriya Za Ta Kece Raini Da Amurka a Poland

Wani wasa da Najeriya ke bugawa da kasar Ingila

Ita dai Amurka za ta kara da Najeriya ne a daidai lokacin da take cikin fushin kayen da ta sha a hannun Ukraine.

Tawagar ‘yan wasan Najeriya ta Flying Eagles, za ta kece raini da ‘yan wasan Amurka, a ci gaba da gasar cin kofin duniya na ‘yan kasa da shekaru 20 da ke gudana a kasar Poland.

Za a buga wasan ne a birnin Bielsko- Biala, a wannan rukuni na D.

Gabanin wannan wasa, Eagles ta lallasa kasar Qatar da ci 4-0, yayin da ita kuma Amurka ta sha kaye a hannun Ukraine da ci 2-1.

Akwai yiwuwar wannan karawa ta zama mai sarkakiya ga 'yan wasan Najeriya, lura da cewa Amurka ba kanwar lasa ba ce.

Ita dai Amurka za ta kara da Najeriya ne a daidai lokacin da take cikin fushin kayen da ta sha a hannun Ukraine.

Ita kuma Najeriya za ta kara ne da burin ganin ta shiga rukuni na gaba, inda idan har ta yi nasara, za ta shiga zangon da-an-ci, an cire ka.