Tsohon Babban Sakataren Majalisar Dinkin Duniya, Kofi Annan ya rasu yana mai shekaru 80.
Ya rasu a wani asibiti da ke birnin Bern a kasar Switzerland da safiyar yau Asabar.
“Cikin yanayi na alhini, iyalan Annan da gidauniyar Kofi Annan na sanar da rasuwar Kofi Annan, tsohon babban Sakataren Majalisar Dinkin Duniya, da safiyar yau Asabar 18 ga watan Agusta, bayan da ya yi fama da ‘yar gajeruwar rashin lafiya.”
Bayanai daga iyalai da gidauniyar tasa, sun nuna cewa, Annan ya rasu ne zagaye da iyalansa.
A sanarwa da ta wallafa a shafinta na Twitter, gidauniyarsa ta kwatanta Annan a matsayin “dattijo mai kishin duniya, wanda ya sadaukar da rayuwarsa wajen tabbatar da zaman lafiya.”
Annan shi ne Babban Sakataren Majalisar Dinkin Duniya na 7, inda ya rike mukamin daga shekarar 1997 zuwa 2006.
Shi ne kuma bakar fata na farko da ya rike wannan mukami.
Ya rike mukamin wakilin Majalisar Dinkin Duniya da Kungiyar Laraba na musamman kan rikicin kasar Syria daga watan Fabrairu zuwa watan Agustan 2012.
An haife shi a birnin Kumasi na Ghana da ke yammacin Afirka a ranar 8 ga watan Afrilun 1938.
Ya rasu ya bar matarsa da 'ya'ya uku , Ama, Kojo da Nina.