Dr Ruqayya Aliyu, malama a jami’ar Bayero ta Kano ta ce tunda ta kwallafa ranta kammala karatun aikin jarida sai da ta cimma burinta ta hanyar naci da jajircewar wajan ganin ta cimma wannan burinta.
Dr Ruqayya ta ce duk da cewar da farko ta nemi gurbin karatu bayan ta kammala karatun sakandire sai aka yi rashin sa’a bata samu damar cin jarabawar JAMB ba, a cewarta hakan bai karya mata gwiwa ba wajen ganin ta cimma burinta, sai ma kara mata kaimi da hakan yayi.
Ta kara da cewa ta nemi gurbin karanta aikin jaridar a jami’ar Maiduguri inda ta nemi diploma bayan gwagwarmayarta sai ta samu nasara aka bata aji na biyu a matakin digiri ta kuma fito a matsayin dalibar da ta fi kowa lashe jarabawa a shekarar da ta kammala karatun ta.
Dr Ruqayya ta ce gamawar ta ke da wuya sai jaridar Dailytrust ta bata aiki kai tsaye inda ta yi aikin jarida na shekaru uku daga bisani ta sake neman gurbin karatu a karo na biyu inda ta kammala, bugu da kari, matashiyar bata tsaya a nan har sai da ta zama Dakta a fannin karatu, wato digirin digirgir.
Dr Ruqayya dai ta ce duk wannan karatu ta yi shi bisa jajircewa da sawa ranta sai ta cimma burinta kuma bata tsaya ko na shekara da yaba sai da ta kamala. Daga karshe dai ta ja hanakalin mata da su daina gajiyawa da zarar sun sa a ransu son cimma wani buri na rayuwa.
Your browser doesn’t support HTML5