Masu magana suka ce duniya juyin-juyi, kwado ya fada ruwan zafi, saboda kuwa abubuwa fa ba sa tafiya yadda ya kamata wa kungiyar kwallon kafa ta Barcelona, a dai-dai lokacin da take gabar karashe kakar kwallonta mafi muni, tun bayan da tsohon Kwac Pep Guardiola ya saitata ta zama daya daga cikin kungiyoyi mafi nasara a gasar kwallon kafa.
Cinye Barca da Real tayi da ci biyu da daya wasan karshe na gasar kofin Copa del Rey larabar nan ya kammala kwanaki takwas da za’a iya cewa wa’adin lalaci da tabarbarewa wa Barca. Jaridar Sports daily ma bugawa tayi ta rubuta “Karnin Nasara Ya Zo Karshe”.
Rabon da a cinye Barca sau uku a jere tun kakar kwallon 2002 zuwa 2003, sama da shekaru 10 kennan. Tambayar anan itace ko ta fara karewa Barca Ne?