Shafin sada zumunta na yanar gizo Twitter ya kwashe tsawon lokaci bai yi garan bawul ga shafin sa ba, amma kamfanin yana tunanin aiwatar da wasu sauye sauye a yadda shafin ke gudana. Shugaban kamfanin Jack Dorsey, ya bayyanar da hakan.
Kamfanin wanda yake kokarin kawo karshen hanyoyi da akanyi amfani da shafin wajen aika kalamun batanci, da labarai marasa asali, amma yazuwa yanzu kamfanin bai ayyanar da hanyoyin da yake kokarin bi ba don gabatar da canje-canjen.
Sauyin da kamfanin yake kokarin kawowa zai bukaci kashe makudan kudade, wanda hakan ba zai wa masu hannun jari a kamfanin dadi ba, kuma kamfanin bashi da karfin kudi irin na kamfanoni kamar su Google da Facebook.
Akwai alamun sauye-sauyen da kamfanin zai samar zai iya shafar yadda mutane ke amfani da shafin wajen sada zumuntar su ta kafar, kamfanin dai bashi kadai ke fuskantar matsalar cin zarafin jama’a ba a kafofin yanar gizo.
Sauyin da kamfanin yake kokarin gabatarwa kan iya magance matsalar satar bayanai, ko isar da sakonin da basu da asali, musamman a yanayi da ake cikin na zabubbuka a fadin duniya, wanda yawancin ‘yan siyasa kanyi amfani da kafar wajen zarge zarge marasa tushe da kausasan maganganu ga abokan hamayyar su.