Al’ummar Mecedonia na kada kuri’a a yau Lahadi kan ko kasar zata sauya suna.
An bukaci yan kasar da sauya sunan kasar su zuwa Macedonia ta Arewa domin kawo karshen ja’in jar da akwa kwashe shekaru masu yawa anayi da makwabciyar kasar Greece, domin share hanyar shigar kasar cikin kungiyar NATO da tarayyar Turai.
Greece ta ce sunan Macedonia mallakin yankin Arewa ne kacokan, wanda amfani da sunan ya nuna niyyar Skopjes na mallakar yankin na Greece.
Tsawon shekaru Greece ta rika takura Skopje da ta sauya sunan kasar, inda ta matsa mata lamba da ta rika amfani da wani sunan na tsohuwar jamhuriyar Yugoslavia ta Macedonia a Majalisar Dinkin Duniya.
Haka kuma ta cigaba da hana karamar makociyar kasar daga samun damar zama mamba a NATO da kuma Tarayyar Turai indai har ta zauna da sunan.
Shugaban kasar Gjorge Ivanov yace yarda da bukatar Greece cin zarafin akidar kasane.”