Hassana Aliyu, mace ce mai lalurar ciwon sikari wacce ta ce tana kokarin bin wasu matakai domin ta tabbatar da sikarin ta bai yi kasa ba domin samun damar gudanar da azumin watan ramadana, a cewarta kafin lokacin ramadana ya kankama takan nemi shawarwari daga wajen liktico gabanin gabatowar wata mai alfarma.
Malama Hasana, ta kara da cewa tana kiyaye dukkanin sharudan da aka gindaya mata sannan tana yawan gudanar da atisaye tare da cin abincin da ya danganci ganye da rage cin abinci da ke dauke da sikari da yawa.
Ta kara da cewa da zarar ta fuskanci cewar sukarin ta yayi kasa da zarar an sa sha ruwa tana cin abu mai sikari ne da zai dago da sikarin tare da daidaita shi.
Hasana ta ce yana da kyau kamar yadda likitocinsu ke fadi yawan shan kayan gwari amma ba masu zaki sosai ba, ta kuma kara da cewa akwai kuma lokutan da suke cin abinci kamar kowa a cewarta idan aka kauracewa abinci mai dauke da sikari a wasu lokutan kan zama illa. Akan haka ne suke surkawa da abincin da kowa ke ci amma tare da kiyayewa
Ku saurari cikakkiyar hira da malama Hassana mace mai lalurar ciwon sikari kuma tana kuma azumi.
Your browser doesn’t support HTML5