Duk da kokarin da hukumomin kasar Nijar suke akan tafiye tafiyen da matasa ke yi zuwa kasashen waje, al’amarin masu zuwa ci rani kasar Algeriya na ci masu tuwo a kwarya, shugaban kundumar Arlit na jamhuriyar Nijar ya ce yanzu haka an sami mutane dari tara da tamanin da daya (981) wadanda aka mayar dasu gida daga kan hanyar su ta zuwa kasar Algeria.
Shugaban ya kara da cewa “akwai jama’a da dama masu tahowa daga yankin jahar Damagaran zuwa arewa, lamarin da yanzu aka mayar da shi fatauci na dan’adam kuma basu da masaniya cewar kasar da zasu tana da wuyar shiga saboda tsaurara matakan tsaro.
Yawancin matafiyan akan dauko su ne sa’an nan a yarda su a hanya idan an kusa kaiwa kasar, ko daga nesa ace masu ga wutar gari can, kuma a cikin sahara hangen wutar wani gari kasan kana iya kwashe tafiyar kilomita talatin ko fiye kafin ka kai wurin wanda yanayin zafi da gajiya da kishin ruwa yake hallaka yawancin su a hanya dan haka wannan lamari yana da ban tsoro da kuma ban tausayi kwarai.
Yanzu haka bayan tawaga ta talatin da bakwai a cikin tawagogin da aka maido su gida, akawai kuma mutane dari tara da tamanin da daya da suka tsallake iyaka aka maido su, da kuma mutane goma sha biyar da sojoji suka gamu da su a hanya wadanda idan aka hada duka adadin su ya kai dari tara da tasa’in da shida (996), yanzu haka ana shirin sallamar su domin komawa gidajen su.”
Daga karshe ya yi gargadi da jan kunnen matasa maza da mata akan gujewa wanan mummunan yanayin rayuwa da jama’a da dama suka sami kawunan su a ciki, sa’annan ya bukaci hukumomi da sauran jama’a su taiamaka wajan wayar da kai dakuma gargadi da jan hankulam matasa domin gujewa irin wannan lamari.