Kisan Wani Sojan Turkiyya Ya Nuna Raunin Yarjejeniyar Da Aka Cimma Da Kurdawa

An kashe wani sojan Turkiyya wani kuma ya jikkata a yau Lahadi bayan wani hari da dakarun kurdawan Syria na kungiyar YPG suka kai a garin Tel Abyad dake arewa maso gabashin Syriar, a cewar ma’aikatar tsaron Turkiyya, duk da cewa an cimma yarjejeniyar tsagaita wuta yayinda mayakan suke janyewa daga yankin.

Ranar Alhamis din da ta gabata ne Shugaban Turkiyya Racep Tayyip Erdogan ya amince da yarjejeniyar tsagaita wutar farmakin da dakarunsa ke kaiwa akan kurdawa ta kwanaki 5 a lokacin wata ganawa da mataimakin shugaban Amurka Mike Pence, don ba mayakan kurdawan damar barin yankin.

A jiya Asabar, an kiyaye yarjejeniyar a bakin iyakar, sai dai wasu ‘yan motocin sojojin Turkiyya da suka tsallaka iyakar, a cewar wani wakilin kamfanin dillancin labaran Reuters dake wurin. Amma harin da aka kai yau Lahadi ya bayyana raunin yarjejeniyar.

Kasar Turkiyya na kallon mayakan kungiyar YPG, wanda sune suka fi yawa a dakarun Syria da kurdawa ke jagoranta, a matsayin ‘yan ta’adda saboda alakar su da mayakan kurdawan dake kudu maso gabashin Turkiyya.