Allah mai hallitta, kowane dan’adam da irin hallittar da Allah yayi mishi. Abun la’akari da shi a nan shine, akwai bukatar kowane mahaluki yayi amfani da baiwar da Allah yayi mishi wajen amfanar da al’umar sa.
A irin hakane wani matashi me suna Abdulsalam Umar me lakani “Adduwa” shidai wannan yaron dan shekaru goma sha uku da haihuwa ne, kuma yana makarantar sakandire, wanda yake taimakama yara a unguwarsu, da abubuwan wasa da kuma hazaka.
Shi dai wannan yaron yakan sarrafa abubuwa da dama don meda su abubuwan da zasu amfananr da yara da kuma sasu sha’awar nuna hazakar su a kowane lokaci, yakan hada mota ta kwali ya kuma samata wani sinadari da ake amfani dashi a radiyo don wannan motar tayi tafiya, akan kuma hada wannan motar da wani maganadisu don tayi waka lokacin da aka kunnata tana tafiya.
Shi dai Adduwa yakan kirkiri abubuwa da dama, wanda ya hada da samar da fanka me amfani da batur wanda ke bada iska. Wannan wata hanya ce da yara matasa zasu iya amfani da baiwar da Allah yayi musu su tallafawa wasu, wanda kuma daga bisani sukan iya zama wasu masu kirkirar abubuwa don cigaban tattalin arzikin kasa. Yakamata duk inda matasa suke suyi kokarin yin amfani da basirar da Allah ya basu don taimakama kansu dama al’umar su baki daya.