Daraktan Kungiyar Kiristocin Syria game da ‘yancin bil’adama, Osama Edward ma ya sanar da cewa, daruruwan Kiristocin da iyalansu ne, suka bar cikin kwaryar garin Sadad zuwa garin Homs da kuma Damascus babban birnin Syria dake karkashin ikon gwamnati.
Sun yi hijirar ne saboda gujewa abin da ka je ya dawo musu, ganin yadda ‘yan kungiyar ISIS ke ta dada kunno kai, zuwa garuruwan da suke da niyyar kai muggan hare-hare. Edward yace, da yawa suna tsoron kar abin da ya faru, na kisan gillar da aka yiwa Kiristocin Kabilar Yazidi ya faru da su.
Kusan kashi 10 daga mutane Miliyan 23 na kabilar Prewar da ke Syria kiristoci ne. Zuwa yanzu dai sojojin taron dangin da Amurka ke jagoranta, sun kai hare-haren sama fiye da sau dubu 6. A jiya 8 ga watan Agustar nan ne, shekara daya cur! da kaddamar da yakar ‘yan kungiyar ta ISIS.