Kiristoci Na Gudanar Da Bikin Kirsimeti A Fadin Duniya

  • VOA Hausa
A yau Laraba Kiristoci a fadin duniya ke gudanar da bikin Kirsimeti domin murnar zagayowar ranar haihuwar Isa Almasihu.

Daga Najeriya zuwa nahiyoyin Afrika da Turai da Asiya da ma Amurka ta Kudu Kiristoci na gudanar da shagulgulan bikin Kirsimeti, fiye da shekaru 2000 bayan haihuwar Almasihu a garin Bethlehem, dake kudancin birnin Kudus.

Kirsimeti, wanda ya rikide zuwa wani biki da ake gudanarwa a duk shekara, lokaci ne na nuna kauna da 'yan uwantaka da bayar da kyaututtuka.

A Najeriya, shugaban kasar Bola Tinubu ya taya 'yan Najeriya murnar zagayowar bikin kirsimeti, inda yace kasar na kan tafarkin farfadowa da ci gaba.

Shugaban kasar a sanarwar daya fitar jiya Talata ya bukaci 'yan Najeriya su yiwa shugabanni addu'o'i a dukkanin matakai.