Paparoma Francis ya yi bukin Ista (Easter) tare da yin addu'a ga masu fuskantar tsanani a sassan duniya
WASHINGTON, DC —
Kirista a fadin duniya na ta shagulgulan wani muhimmin fanni na Kiristanci, wato Ista (Easter), wanda tuni ne na mutuwa da kuma tashin Yesu Almasihu daga matattu bayan kwanaki uku.
Paparoma Francis ya jagoranci sujjadar ta Easter ne na salon Katolika a Dandalin St. Peters. Ya yi addu’ar kawo karshen fama da Kirista ke yi, ya na mai addu’a ga daliban da kungiyar al-Shabab ta hallaka a jami’ar Garissa da ke Kenya.
A Birnin Kudis dubban Kirista sun taru a wurin da yawancin Kirista su ka yi imanin cewa nan ne aka gicciye tare da binne Yesu Almasihu.