"Ki Bayyana Kudade Da Aka Kwato Daga Hanun Barayin Gwanatin Tun 1999"-Inji 'Yan Gwagwarmaya.

Mutane a wata kotun Najeriya

Ina Kudaden da aka dawowa Najeriya daga ajiyar irinsu su shugaba Abacha tun 1999?

Wata kotun tarayya a Legas, ta yanke hukunci kan karar da wata kungiyar kare demokuradiyya mai suna SERAP ta shigar, wcce ta nemi gwamnatin tarayya ta bayyana dukkan kudaden da ta kwato daga hanun marasa gaskiya tun 1999, shekarar da Najeriya ta koma bin salon mulkin demokuradiyya.

Gwamnatocin tarayya tun zamanin Obasanjo, sun sha yin shelar miliyoyin Dala da suka kwato, ko aka dawowa Najeriyadas su daga ketare, kudade da ake zargin tsohon shugaban Najeriya Janar Sani Abacha da danginsa, da wasu jami'an gwmnati suka wawura.

Irin wadannan kudaden ne kungiyar SERAP, ta nemi kotu ta umarci gwmnatin tarayya ta fadawa duniya nawa ne Najeriya ta kwato kuma ina suke?

Da yake tsokaci kan wannan hukunci,daya daga cikin shugabannin kungiyar da take rajin kare salon demokuradiyya, Democratic Action Group da turanci, Mallam Mustapha Yahya, yace wannan hukunci, nasara ce ga tsarin demokuradiyya.

Yace akwai bukatar gwamnatin tarayya ta mutunta wanan hukunci.

Ga karin bayani.

Your browser doesn’t support HTML5

Hukunci kan kudaden da Najeriya ta kwato