Kiwon Lafiya: Za a Kashe Dala Miliyan 200 a Kasashen Yammacin Afrika

Wata Mata Da 'Yar ta Da Ke Fama Da Rashin Lafiya

An ware akalla kudi miliyan 200 na dalar Amurka domin taimakawa wajen inganta lafiyar mata da kula da kananan yara tare da samar da ilimi mai nagarta a wasu kasashen Yankin Sahel da ke Afrika.

Kasashen sun hada da Jamhuriyar Nijar, Mali, Chadi, Maurtitania, Ivory Coast da kuma Burkina Faso.

A cewar Dr. Fatimatou Mousa, kwararriya a fannin tsarin iyali, ta ce wannan shiri zai taimaka wajen baiwa mata da yara kanana ‘yan cinsu a lokacin rayuwarsu.

“Wannan shiri zai baiwa mata damar biyan bukatunsu da samun ‘yan ci wanda hakan zai tamaka wajen samun biyan bukatun kansu.” In ji ta.

A shekarar 2013 da Sakatare na Majalisar Dinkin Duniya, Ban ki moon, ya kai ziyara kasar Nijar ne, hukumomin kasar suka nemi a tallafa musu domin biyan wannan bukata in ji Ministar al’umar Nijar, Madame Mai Chibi Kadijatou Dandobe.

“Yaro ya kamata a bashi abinci mai kyau a bashi tarbiya, ya kuma kamata a ce akwai likita idan akwai wata matsala domin kasashen Sahel matsalolinsu duk daya.”

Shi dai wannan tallafi zai zo ne daga Bankin Duniya.

Ga karin bayana a rahoton Souley Moumouni Barmah:

Your browser doesn’t support HTML5

Kiwon Lafiya: Za a Kashe Dala Miliyan 200 a Kasashen Yammacin Afrika- 2’34”