An tura tawagar wakilai daga gwamnatin Italiya da Jamus, wato kasar Paparoma Benedict ta asali.
WASHINGTON, DC —
Paparoma Francis ne zai jagoranci taron jana'izar tsohon Paparoma Benedict a dandalin St. Peter's ranar Alhamis. A ranar Asabar ne dai Paparoma Benedict ya rasu yana da shekaru 95 a duniya.
Sauran shugabanni da suka hada da sarki da sarauniyar Belgium, da sarauniyar Spain, da shugabannin kasashe kusan 13 za su halarci taron. Jakadun yawancin kasashe ne zasu wakilci kasashensu a fadar Vatican.
Tun a ranar Litinin aka ajiye gawar Paparoma Benedict a majami’ar St. Peter's Basilica, inda sama da mutane 160,000 suka je yi masa bankwana ya zuwa ranar Laraba da rana.