Kimanin matasa hamsin ke samun horo a fannoni daban daban na koyon sana’oi, a jihar Abia, karkashin wani shirin “Vicar Hope Foundation Springs Board Skills Acquisition Program” na matar Gwamnan jihar Mrs. Nkechi Ikpeazu.
A cewar matar Gwamnar shirin na hadin guiwa ne da hukumar mai na jihar Abia, da hukumar samar da aikin yi na Gwamnatin Najeriya, watu NDE, kuma shirin wani yunkuri ne na rage zaman kasha wando a tsakanin matasa a jihar.
Da take kadamar da shirin a Obehie, a karamar hukumar Ukwa ta kudu, matar Gwamna ta bukaci matasan dasu sa ido akan abubuwan da za’a koya masu domin ya kasance abinda zasu dogara da zai canja masu rayuwa.
A nashi jawabin kwamishinan matasa na jihar Haglar Okorie, wanda kuma shine shugaban taron ya ce Gwamnatin jihar a shirye take wajan ganin cewa ta samarwa matasa aiyukan yi.