Duk da cewa ba gwajin makaman kare dangi bane, ko gwajin Nukiliya aka yi ba, to amma shagalin da Koriya ta Arewa ta shirya na gabatarda wani sabon jirgin ruwanta.
Mai tafiya karkashin teku, na nuna cewa kasar ta yi haramar ci gaba da kara matsin lamba akan Amurka, a dai-dai lokacinda ake fuskantar cikas wajen sake maida kasashen biyu akan teburin tattaunawa.
A yau Talata ne tashar talabijin ta kasar Koriya ta Arewa ta nuna wasu hotunan shugaba Kim, na duba wani sabon jirgin karkashin ruwa, ya na kuma cewar bada jimawa ba wannan sabon jirgin yakin zai fara shawagi a tekun gabashin Koriyar.
Koda yake bayanai basu fayyace irin makaman da jirgin ruwan ke dauke da su ba, ana kyautata zaton cewa mai yiyuwa ne ana iya dora mishi makaman nukiliya masu linzami.