Kila Wasu 'Yan Najeriya Ba Zasu Buga Wasan AFCON Ba

Wasu daga cikin zaratan kwallon Najeriya na fama da rashin Lafiya.

A yayin da ake shirye shiyen fara gasar cin kofin kwallon kafa ta Nahiyar kasashen Afrika AFCON 2019 a can kasar Masar.

Akalla ‘yan wasan kungiyar kwallon kafa ta Super Eagles a Najeriya su 10 ne yanzu haka ke jinya gabanin fara gasar ranar juma’a 21 ga watan Yunin 2019.

Bayan haka a ranar Asabar 22 ga watan nan ne Najeriyar za ta fara wasanta na farko inda za ta fafata da kasar Burundi.

Wasu rahotanni na nuni da cewa rashin lafiyar ‘yan wasan na da alaka da iskar da suka shaka ta na'urar sanyaya daki a wani otel.

A cikin 'yan wasan da abun ya shafa sun hada da Ahmed Musa, Leon Balogun, Shehu Abdullahi, Henry Onyekuru sai kuma Chidozie Awaziem.

Rashin lafiyar wadannan ‘yan wasa babban kalubale ne ga wasannin da ke
gaban Najeriya, a gasar bayan rashin nasarar su a hannun Senegal da kwallo daya da nema ranar Lahadi a wasan sada zumunci da sukayi.