Kenya-'Yansanda Sun yi Amfani Da Borkonon Tsohuwa Kan 'Yan Zanga-Zanga.

Wani mai goyn bayan 'yan hamayya dauke da adda a unguwar talakawa da ake kira Kawangware dake birnin Nairobi.

Lamarin ya auku ne a birnin Nairobi a gundumar Kawangware indi galibin mazauna yankin marasa galihu ne.

A Kenya 'Yansanda sun yi amfani da borkonon tsohuwa domin tarwatsa masu zanga zanga a wata gundumar da ake kira Kawangware dake birnin Nairobi, inda galibin mazauna wurin talakawa ne, kwana daya bayan wuta kone darurwan masana'antu da wuraren kasuwanci, kuma mutane dauke da adduna da sanduna suka wawushe kantuna da gidaje.

Matasa wadanda galibi suke goyon bayan shugaban 'yan hamayya Ra'ila Odinga, suna takalar 'Yansanda, sannan su gudu su buya domin kaucewa hayakin-mai sa-hawaye, wani mai goyon bayan Odinga ya yace "babu alamar wanan lamarin zai yi sauki cikin wani dan karamin lokaci," daga nan ya zargi hukumar zaben kasar da tafka magudi.

Tarzomar da ta auku jiya ta samo asali ne lokcinda jita-jita ta fara bazuwa cewa, wasu 'yan banga na kabila kikiyu da ake kira "Mungiki" sun shigo yankin. Bangar ta yi kaurin suna wajen datse gabobi da kuma dandake wadanda suka fada hannunta, kuma ita ake azawa alhakin kisan daruruwan mutane a rikicin siyasar kasar da aka yi a shekara ta 2007.

Shugaban hukumar zaben kasar yayi alkawarin zai bada karin bayani kan makomar zaben, duk da cewa ba'a yi zabe ba a wasu sassan kasar, wanda ya tilastawa hukumar ta dage zaben har illa ma sha'allahu, saboda dalilan tsaro.