Kenya: Mutane Zasu Iya Yiwa Kansu Gwajin Cutar Kanjamau

Kasar kenya ta shiga sahun kasashen da suka gabatar da tsarin gwajin cutar kanjamau da mutum zai gudanar da kansa, da nufin karfafawa mutanen guiwa su yi gwaji domin tantance ko suna dauke da kwayar cutar ko babu.

Gwamnati tayi kiyasin cewa, akwai kimanin mutane dubu dari biyar a kasar Kenya da suke dauke da kwayar cutar kanjamau ba tare da sun sani ba.

Akwai na’urorin gwajin iri biyu, da irin wadda ake gogawa a baka da kuma na gwajin jinni.
Ana sayar da na’urar gwada jinin ne a kan kudin kasar Kenya, Kenyan shillin dari takwas da hamsin kwatankwacin dala takwas. Yayinda ake sayar da na’urar gwajin ta baka kwatankwacin dala tara.

Hukumomi sun bayyana cewa an gabatar da shirin ne domin wadanda basu samu aka gwadasu ba, musamman maza da matasa, su iya gwada kansu.