Biyo bayan matakin da madugun 'yan adawar kasar Kenya, Raila Odinga ya dauka na janyewa daga takarar shugaban kasa da za a sake gudanarwa a watan da mu ke ciki, yanzu masana harkar zabe na kasa da kasa na ganin akwai abun dubawa.
Barrister Kassim Gana Gaidam, masanin harkar zabe na kasa da kasa wanda kuma wanda shine sabon kwamishinan hukumar zabe ta INEC a jihar Adamawa,, yace akwai hadari game da matakin da madugun adawar na Kenya ya dauka.
Shima dai wani masani, Abdullahi Prembe, yace akwai bukatar ‘yan siyasar Afrika su dauki darasi daga zaben shekarar 2015 da aka yi a Najeriya.
Hukumar zaben kasar Kenyar dai ta bayyana shugaban kasa mai ci a yanzu, Uhuru Kenyatta, a matsayin wanda ya yi nasara a zaben da ya gabata, da kuri'a miliyan 1.4.
Tuni dai kotun kolin kasar ta yanke hukuncin cewa a ranar 26 ga wannan watan na Oktoba ne za’a sake zaben.
Ga rahoton Ibrahim Abdulaziz da karin bayani.
Your browser doesn’t support HTML5