Allah daya gari ban-ban, a Kenya, a gefe daya ana murna, gefe daya kuma ana zanga zanga, bayan da hukumomin kasar suka ayyana shugaban kasar Uhuru kenyatta, a zaman wanda ya lashe zaben shugabancin kasar.
An goce da zanga-zanga a daren jiya jumma'aa yankunan madugun 'yan adawa Ra'ila Odenga yake da karfi. An ji karar tashin bindiga a babbar unguwar marasa galihu da ake kira kibera dake Nairobi, har da ma wasu sassan birnin inda talakawa suka fi karfi, da kuma birnin Kisimu dake yammacin kasar.
Shaidun gani da ido suka ce 'Yansanda sun harba borkono mai sa hawaye a wata unguwar talakawa da ake kira Mathare, yayind a jiragen 'Yansand a masu saukar ungulu suke shawagi a sama.
Amma kuma sabanin wannan yanayi ne a unguwnanin da shugaba mai ci Uhuru kenyatta yake da rinjaye magaoya bayans a suka fantsama kan tituna suna busa algaita da ake kira Vuvuzela, suna kada tutoci, suna murnar sakamakon zaben.
Tunda farko a jiya jumma'an, masu sa ido da 'yan jarida,'yan siyasa da wakilan jam'iyu a rumfunan zabe, sun cika makil a wani zaure inda shugaban hukumar zaben na kenya Chibukati ysa ayyana shugaban kasar mai ci a zaman wanda ya sami nasara a zaben.
Babban jami'in hukumar zaben yace, shugaba Uhuru kenyatta, ya sami kuri'u milyan 8,203,290, wand a shine kashi 54.27, yayind a abokin karawarsa, Ra'ilda zodinga, ya sami 44.74, watau kuri'u milyan 6,762, 224.