Kazamin Fada A Garin Kobani

Hayaki bakikirin a garin Kobani

A yau Lahadi ma an gwabza mummunan fada a garin Kobani na Syria dake kan iyaka da Turkiyya

An bada labarin gwabza wani kazamin fadan a ciki da kewaye birnin Kobani na kasar Syria wanda ke kan iyakar Turkiyya.

An ga hayaki bakikirin na tashi daga birnin a yau Lahadi a daidai lokacin da Kurdawa mayaka ke fadan kare birnin daga hare-haren 'yan Daular Islama.

Jiragen saman yakin kawancen taron dangin da Amurka ke jagoranta su na ta luguden wuta a cikin Kobani da kewaye.

Sojojin kasar Turkiyya su na nan kawai a tsaye a tsallaken kan iyakar duk kuwa da karuwar kiraye-kiraye da matsin lambar da kasashen duniya ke yiwa shugaban kasar Turkiyya Receb Tayyip Erdogan cewa ya kai dauki.

Jami'an Majalisar Dinkin Duniya dake yankin sun yi kashedin cewa idan aka ci birnin Kobani da yaki, ba Allah Ya kiyaye za a murkushe Kurdawan da yawan su ya kai dubu goma sha biyu a cikin su har da daruruwan tsofaffi a tsakiyar birnin, kuma a yi mu su kisan gilla. Kungiyar lura da hakkokin bil Adama a kasar Syria ta ce da safiyar jiya Asabar mayakan Daular Islama ne ke rike da kashi Arba'in cikin dari na garin na Kobani.

Ya zuwa yanzu dai gwamnatin kasar Turkiyya ta ki shiga fadan, ta na mai ambaton dangantakar dake tsakanin Kurdawan dake kare garin Kobani da haramtacciyar jam'iyar 'yan kwadagon Kurdistan, PKK a takaice, wadda ta yi shekara da shekaru ta na tawayen neman mulkin kai a kudu maso gabashin kasar Turkiyya, wadda kuma gwamnatin Turkiyya da ta Amurka suka sa a jerin kungiyoyin ta'addanci.

Sojojin Turkiyya a kan iyakar su da Syria