WASHINGTON D.C. —
Gwamnatin kasar Kazakhstan na nazarin kakkaba dokar kulle a ranar 5 ga watan Yuli bayan da aka kara samun adadin masu kamuda da cutar a kasar.
Wannan ne karo na biyu da kasar za ta shiga yanayi na kulle sakamakon Cutar Coronavirus.
Shugaban kasar Kassym-Jomart Tokayev ne ya bayyana wannan matakin kuma ya ce wata hukuma ta musamman za ta stara yadda za a fara kullen.
Tokayev ya umarci gwamnatinsa da ta kara karfafa matakan takaita yaduwar cutar bayan da adadin masu cutar a kasar ya ninka sau bakwai jim kadan bayan an cire wasu matakai a tsakiyar watan Mayu.