Biyo bayan dage zaben da aka yi, yanzu haka jami'an zabe sun dukufa domin kammala ayyukan da suka kamata,tare da ba da tabbacin biyan ma'aikatan da aka dauka hakkokinsu.
Yanzu haka jami'an zabe a jihohi sai kara daura damara da zage damtse suke yi,don ganin ba'a sake samun cikas ba a ranar Asabar, da aka sa domin gudanar da zaben.
Kawo yanzu wasu kayakin da ba su isa wasu jihohi ba,tuni suka iso inda hukumar zabe ke zuwa babban bankin Najeriya, CBN, domin diban kayayyakin da suka ison.
Barr. Kassim Gana Gaidam,da ke zama kwamishinan zabe a jihar Adamawa, daya daga cikin jihohin da aka samu jinkiri a wasu yankunanta,ya bayyana matakin da aka dauka.
"Sai dai mu yi fata wannan canji da ya faru ya zama alheri, kuma ya zama zaben mun samu mun yi shi kamar yadda ya kamata." Inji Gaidam.
Haka nan kuma, kwamishinan zaben ya bayyana irin matakin da aka dauka, idan har wasu ma'aikatan wucin gadin suka ki komawa domin gudanar da zaben.
Saurari rahoton Ibrahim Abdulaziz domin jin cikakken bayani:
Your browser doesn’t support HTML5