Wasu matasa sun ce sun shiga shayeshaye ne saboda dauke kewa da bacin rai kan irin rashin da su ke fama da shi. Su ka ce sam ba su jin dadin garin, saboda hatta iyayensu a wahale su ka taso. Don haka su ka ce kwayar ce kawai ke kwantar masu da hankali. Don haka muddun babu ita to babu zaman lafiya.
Wakilinmu na Kano da ya yi hira da matasan Mahmud Ibrahim Kwari ya ce baya ga matasan da ke kafa hujja da rashin ayyukan yi, hatta wasu manyan mutane ciki har da ‘yankasuwa da ma’aikatan gwamnati da matan aure na ta’ammali da kwayoyi bisa dalilai dabandaban.
To saidai Dakta Musa Gambo Takai na Sashin Kula Da Masu Lalurar Kwakwalwa na Asibitin Koyarwa na Aminu Kano ya zayyana illolin amfani da duk wani kayan maye. Illolin sun hada da na kwakwalwa da ciwon hanta da ciwon hanta da ciwon matuwa da shanyewar jiki da kuma nakkasa jariri (ko dan tayi) gabanin haihuwarsa. Wannan kuwa bayan ga yawan haddasa hauka ne da kwayoyin ke yi, in ji shi.
Your browser doesn’t support HTML5