Rabiu Sai’du Yusuf wanda aka fi sani da RC Top, mawakin Hausa hip-hop wanda ya ce sha’awa da ra’ayi ne ya sa ya zabi fannin waka na hip-hop, duba da yadda matasa suka raja’a ga wakokin hip-hop na kasashen waje.
Wakokinsa na karkata ne da yanayin da ya tsinci kansa, walau na yanayin kasa ko al’adunmu, inda a mafi yawan lokkutta ya kan fito da kasar sa ko al’adun ta, ta hanya wake abinda yake so.
Alal misali a wata wakarsa ta Kano ta dabo, ya bayyana yadda aka kirkiro sunan jihar Kano, kofofin Kano da ma sana’o'in da aka san mutanen Kano da ita, ta hanyar bayyana su a wakensa.
RC top ya ce, a wakarsa tana nusar da al’umma da yadda suka rungume al’adarsu, suke kuma kauracewa wasu dabi’un da ba ta su ba, a cewarsa kayan aro baya rufe katara, waka wata hanya ce ta bada labari, tarihi da makamantansu na wata alumma.
Akwai wata waka ta 'Ku Ruko ta ’ waka ce da yake nuna yadda wasu 'ya'ya mata suke shiga mumanan dabi’u, suke kuma kauracewa iyaye ta hanyar shan miyagun kwayoyi, da wasu dabiu da basu dace ba, a karshen suke shiga wani hali na ha’ula’I duk da zummar nusar da matasa illar yin ire-iren wannan dabi’u da kuma makomar masu yin hakan.
Ya kan waiwaye 'yan siyasa mussaman ma, a yanzu da ake kakar siyasa da yadda suke yaudarar al'umma kafin su sami madafar mulki, da zarar sun samu sai labari ya sauya.
Babban damuwar RC TOP dai yace shine wasu mawaka basa duba batutuwan da suke isar da sakonnin ko fadakarwa, maimaikon hakan suna waka ne kawai ba tare da sun nufi wata alkibila ba.
Your browser doesn’t support HTML5