Babbar jam’iyyar adawa ta PDP a Najeriya ta gudanar da taronta na farko tun bayan gudanar da babban zabe na kasa. A taron, wanda ya sami halartar wasu jam’iyyun adawa guda bakwai, an zabi gwamnan jihar Bauchi, Senata Bala Abdulkadir Muhammed (Kauran Bauchi) a matsayin sabon shugaban kungiyar gwamnonin PDP a Najeriya.
Gwamnonin jihohin da PDP ke mulki da zababbun wakilai na tarayya, da kuma jam’iyyun adawa guda bakwai sun halarci taron, wanda ke bukatar jam’iyyun adawa su hada kai don kawo sauki ga al’ummar Najeriya a cewar Honarabul Ali Isa Jese, wanda yayi bayani a matsayinsa na sakataren kungiyoyin jam’iyyun Najeriya.
Honorabul Bappah Misau, dan majalisar wakilai daga jihar Bauchi, ya bayyana dalilan da su ka sa aka zabi gwamna Bala na jihar Bauchi, a matsayin shugaban kungiyar Gwamnonin jihohin Najeriya da ke karkashin mulkin jbabbar jam'iyyar adawa ta PDP.
Sabon Shugaban kungiyar gwamnonin PDP a Najeriya din, Senata Bala Abdulkadir Muhammed, ya ce zaben da aka yi musu da mataimakinsa na nuni da irin ayyukan dake gabansu na habaka jam’iyar PDP a Najeriya don ci gaban kasar da 'yan kasar baki daya.