Gwamnatin jihar Katsina da ke arewa maso yammacin Najeriya, za ta kafa turakun fitilu 7,240 akan hanyoyin da makiyaya ke bi har na nisan tafiyar kilomita 905 domin a kaucewa rikicin makiyaya da manoma a jihar.
Jaridar Daily Trust ce ta wallafa labarin a shafinta na yanar gizo na ranar Lahadi tana mai cewa, Shugaban kwamiti na musamman da aka kafa kan hadin kan manoma da makiyaya, Alhaji Abdulaziz Lawal ne ya bayyana hakan a wata sanarwa da ya fitar a ranar Asabar.
Lawal ya ce, za a kafa turakun fitilun a hanyoyin da makiyaya ke bi da suka ratsa cikin yankunan Ingawa, Jibia, Batsari, Safana, Danmusa, Kafur, Faskari, Zango da Baure na kananan hukumomin jihar a matakin farko a cewar jaridar ta Daily Trust.
Ya kara da cewa, za a kammala zangon farkon wannan aiki a cikin makwanni shida, yana mai jaddada cewa, an dauki matakin ne domin a samarwa makiyaya hanyoyin wucewa cikin sauki.
A cewar shi, hakan zai taimaka wajen kare rikicin makiyaya da manoma.
Rikicin makiyaya da manoma a ‘yan watannin baya-bayan nan, ya haddasa mutuwar daruruwan mutane a jihohin Benue, Pilato, Nasarawa, har da ma wasu jihohi da ke kudancin Najeriya.
Ya kuma haddasa rarrabuwar kawuna a tsakanin al’umomin da suka kwashe shekaru aru-aru suna zaman lafiya.