Katsalanda Ce Ga 'Yan Sanda Su Nemi Kama Kassim Afegbua

Ibrahim Babangida

An bukaci jami'an tsaro a Najeriya da su rika nesanta kawunansu da abubuwan da ba a nemi su shiga ba, don kare mutuncinsu da kuma tabbatar da bin doka da oda.

Masana shari'a da masu fashin baki da kuma 'yan jarida su na bayyana damuwa a kan katsalandar da 'yan sanda suke neman yi ne a batun cacar baki game da wasikar da aka ce tsohon shugaba Ibrahim Babangida ya rubuta, wanda daga bisani yace shi bai rubuta ba. Rundunar 'yan sandan ta Najeriya ta ayyana cewa tana neman Kassim Afegbua, kakakin tsohon shugaban, ruwa a jallo.

Barrister Sunday Joshua Wigra, yace wuce gona da iri ne ga 'yan sanda su bukaci Kassim Afegbua da ya bayyana kansa ko kuma zasu je su kama shi, tun da tsohon shugaba Ibrahim Babangida bai kai kararsa a kan cewa yayi masa kazafi ba.

Yace daukar irin wannan matakin da 'yan sanda ke neman yi domin kawai su dada ma wasu a kan mulki, abu ne da ka iya gurgunta bin doka da oda, yana mai cewa ai shi Kassim Afegbua ya san inda yake masa zafi.

Daya daga cikin editocin jaridar Leadership Newspapers ta Najeriya, Muhammad Isma'il, yace wannan cacar-baki ba ta ba su mamaki ba, amma suna mamakin yadda jami'an tsaro suke neman cusa kansu cikin lamarin.

Ya bukaci jami'an tsaron da su rika nesanta kawunansu da irin wadannan abubuwan.

Your browser doesn’t support HTML5

Jami'an Tsaro Su Tsame Hannu A Rikicin Wasikar Babangida - 1'44"