Fitacciyar ‘yar wasan ninkaya nan ta Amurka, Katie Ledecky, ta kawar da tarihin da ta kafa a duniya a fagen ninkaya, ta hanyar lashe kyautar Zinare bayan da ta kafa sabon tarihin a ninkayar tsawon mita 400 a gasar wasannin motsa jiki da ake yi ta Olympics a birnin Rio da ke Brazil.
WASHINGTON DC —
‘Yar shekaru 19, Ledecky ta taba bangon karshe cikin mintina uku da dakikoki 56, wanda ya kawar da tarihin da ta kafa ya kuma ba ta damar lashe kyautar zinaren ta a karon farko a gasar.
A daya bangaren maza kuwa, Adam Peaty na kasar Burtaniya shima ya kafa tarihi a ninakyar tsawon mita 100 cikin dakoki 57, wanda hakan ya ba shi damar lashe kyautar Zinare.
Tawagar Amurka da ke halartar gasar sun sami kyautar zinare a ninkayar yada-kanin-ka, ko kuma mika ka huta, inda Michael Phelps ya lashe kyautar zinarensa ta 19, wanda hakan ya bashi damar zama dan wasan motsa jiki da aka fi karramawa da kyautar a zinare a gasar ta Olympics.